Gobara Ta Lakume Hatsi Na Miliyoyin Nera a Garin Gombe

Gwamnan jihar Gombe Ibrahim Dankwambo

Gobara ta lakume kayan hatsi na miliyoyin nera a kasuwar tudun hatsi dake garin Gombe.
Gobarar ta lakume hatsi a kasuwar tudun hatsi dake Gombe. Gobarar ta fara ne wajen karfe uku na daren jiya. Kasuwar tudun hatsinGombe tana tsakiyar garin ne.

Shugaban kasuwar Alhaji Usman Adamu ya shaidawa wakilin Muryar Amurka Abdulwahab Muhammed yadda wutar ta faru. Yace wutar ta samo asali ne daga wutar lantarki. Sama da shaguna dari biyu suka kone. Yace an yi asara miliyoyin nerori. Ba da dadewa ba zasu zauna su tantance ko asarar nawa aka yi. Yace mutane na zuwa daga Chadi, Niger, Ghana da ma wasu kasashen sayen hatsi a kasuwar.

Yan kwana-kwana sun kawo doki da tankuna uku wadanda suke debo ruwa dasu, suna kaiwa suna dawowa. Sun hada da sawo ruwa suna zubawa cikin motar 'yan kwana-kwana mai inji tana fesawa domin kashe wutar. Yace kwamishana mai kula da ayyukan musamman da babban sakatarensa sun ziyarci kasuwar. Ya kuma gaya masu cewa mai girma gwamnan jihar yana nan tafe.

Hukumar agaji ta gaggawa ta jihar Gombe a karkashin jagorancin Hajiya Laraba Ahmed Kawu tare da wasu ma'aikatan hukumar sun kai ziyarar gani da ido. Tace sun zo ne su ga abun da ya faru, su rubuta rahoto kana su bada shawara akan abun da yakamata a yi. Tace hukumar ce ke baiwa gwamna shawara akan irin taimakon da yakamata a bayar. Ta bada tabbacin cewa gwamnan jihar zai basu agaji.

Kakakin hukumar kwana-kwana Malam Haruna Wambai yayi bayanin irin ayyukan da suka gudanar wajen shawo kan matsalar gobarar. Tun wajen karfe uku suka isa kasuwar kuma sun ci nasarar shawo kan gobarar.

Ga rahoton Abdulwahab Muhammed.

Your browser doesn’t support HTML5

Gobara Ta Lakume Hatsi Na Miliyoyin Nera A Garin Gombe - 3 58"