Gobara Ta Hallaka Mutum 66 A Turkiyya

Otel din Kartalkaya a Bolu

Biyu daga cikin wadanda suka mutu sun rasa rayukansu ne a lokacin da suka duro daga benen don tsira da ransu.

Ministan Ciki gida na Turkiyya ya ce wata gobara da ta tashi a wani otel da ke wajen wani wasan dusar kankara ta yi sanadin mutuwar mutum 66.

Ali Yerlikaya ya ce akalla mutum 51 sun jikkata a ibtila’in wanda ya auku a ranar Talata.

Wutar ta tashi ne da misalign karfe 3:30 na safe a dakin cin abinci da ke otel din Grand Kartal mai bene 12 a wajen wasan dusar kankara na Kartalkaya a Lardin Bolu a cewar jami’ai da rahotanni.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton babu bayanai kana bin da ya haddasa gobarar.

Biyu daga cikin wadanda suka mutu sun rasa rayukansu ne a lokacin da suka duro daga benen don tsira da ransu.

Hukumomi sun ce ana tsare da mamallakin otel din da wasu ma’aikata uku don gudanar da bincike.