ZABEN2015: Gobara Ta Hallaka Kwamishinan Zaben Kano

Shugaban Hukumar Zabe ta INEC Farfasa Attahiru Jega a Abuja, Maris 30, 2015. (File Photo)

Gobara ta hallaka kwamishinan hukumar zabe ta Kano a Arewacin Najeriya, Alhaji Mikail Abdullahi, tare da mai dakinsa da kuma biyu daga cikin ‘yayansu.

Da misalin karfe hudu na asubahin Juma’ar nan ne gobarar ta tashi a gidan kwamishinin da ke rukunin gidaje na kusa da gidan gwamnatin Kano. Wakilin Muryar Amurka Mahmud Ibrahim Kwari ne ya garzaya inda ya dauko mana rahoton faruwar lamarin.

Rahotanni sunce wutar ta samo asali ne daga injin da ke bada hasken wutar lantarki a gidan. Lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar kwamishinan Alhaji Mikaila Abdullahi da matarsa Hajiya Magajiya mai shekaru 31 da ’yayansu Husna mai shekaru hudu sai Amira ‘yar shekaru biyu da haihuwa.

Jami’in yada labaran hukumar zaben jihar Kanon, Garba Lawan ya tabbatar da aukuwa lamarin ga wakilinmu. Yace, bayan tashin gobarar sai da aka garzaya da Alhaji Mikaila Abdullahi tare da iyalan nasa zuwa asibitin kwararru na Murtala da ke Kano, inda a nan ne suka rasu.

Shima kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ASP Magaji Musa ya tabbatar da hakan, yana mai cewa, jami’an za su gudanar da bincike game da lamarin.

Your browser doesn’t support HTML5

Gobara Ta Hallaha Kwamishinan Zaben Kano - 2'24"