Kasar Girka ta idar da shirin nan na aiwatar da tsauraran sharuddan bashin da aka ba ta, na tsuke bakin aljuhu.
Kammala wannan shirin wani babban cigaba ne ga kasar ta Girka, to amma har yanzu da sauran jan aiki ga kasar na yadda za ta farfado da tattalin arzikinta.
Ofishin Firaminista Alexis Tsipras ya bayyana bashi na karshe na makon jiya karkashin wannan tsarin da cewa shi ne abin da ya kira “karshen wani al’amari tamkar wasan kwaikwayo. Yanzu za a iya bude wani sabon babi na cigaba, da adalci da kuma bunkasar tattalin arziki.”
Sannu a hankali dai tattalin arzikin Girka na farfadowa, bangaren yawon bude ido ya bunkasa da kashi 17% a birnin Athens a wannan shekarar, kuma rashin ayyukan yi da yayi tsananin da ba a taba gani ba a baya, a yanzu ya fara zama tarihi.