Girka bata dauki matsayi akan yarjejeniyarta da Tarayyar Turai kan 'yan gudun hijira ba

Tashar jiragen ruwa ta Mytilini: Daga yau Litinin kasar Girka zata fara tasa keyar 'yan gudun hijira zuwa Turkiya

Sa’oi kafin a fara kwashe ‘yan gudun hijirar da ke tsibirin Lesbos. Jami’an kasar Girka ba su karkare matsayar yarjejeniyar tsarinsu tsakaninsu da kungiyar Tarayyar Turai da Turkiyya ba.

Masu fafutuka sun tsara yin zanga-zanga a ranar Litinin, ranar da hukumomin Girka da taimakon daruruwan ‘yan sandan tsaron kan iyakoki daga kasashen Turai za su tasa keyar bakin daga sansanin ‘yan gudun hijirar da ke birnin Mytilini zuwa bakin tekun da jiragen ruwa ke jiransu zuwa Turkiyya.

‘Yan gudun hijirar dai sun bullo daga kasashen duniya daban daban, inda suka sauka ta kan teku a kasar Girka ba bisa ka’ida ba, su kuma jami’an kasar suka tsare su a nan bayan hukumomin sun ki basu mafaka bisa abinda suka ce ba su cancanta ba, sannan hukumomin Girka da cibiyar ayyukan kan iyakokin Turai mai suna Frontex ba su bada wasu cikakkun bayanan aikin kwashe ‘yan gudun hijirar ba.

Wanda hakan ya sa masu fafutukar kare hakkin bil’adama suka musu ca da cewa cin mutuncin dana dam ne kai bakin zuwa Turkiyya inda za su iya fuskantar barazanar rayuwa. Wani jami’in Girka ya fadawa Muryar Amurka cewa Turkiyya fa basu shirya wannan aiki ba, wanda su kuma Turkiyyar suka musanta.