Girgizar kasa mai maaunin 6.7 na rikta ta auku ne kusa da iyakar kasar da kasashen Bangladesh da Myanmar wadda kuma tayi sanadiyar mutuwar mutane tara tare da jikata wasu da dama.
Rahotanni dake fitowa daga kasar sun ce gudaje da dama suka ruguje.
Mazauna birnin Guwahati dake jihar Assam sun fantsama kan tituna yayinda gidajensu suka soma girgizawa saboda litattafai da kayan dake kan ragaya suna ta fadowa. Mutanen sun fice daga gidajensu ne a kokarin tserewa da rayukansu.
Girgizar kasar da ta samo asali a wani yanki mai tazarar kilomita 30 daga arewa maso yammacin birnin Imphal ne ta haka ramin da zurfinshi ya kai kilomita 55.
An ji girgizar a wurare masu nisa kamar Kolkata a yammacin jihar Bengal mai tazarar kilimita 600 a kudu maso yammacin kasar. A kasar Myanmar ma girgizar ta kai babban birnin kasar wato Yangon dake da tazarar kilomta 1176 daga kudancin Indiya.