Girgizar Kasa Ta Aukawa Gabashin Amurka

Jama'a da suka fito daga cikin gine gine da suke aiki,bayan aukuwar girgizar kasa.

Girgizar kasa mai karfin awo 5.9 ta girgiza galibin jihohi dake gabar teku a gabashin Amurka.

Girgizar kasa mai karfin awo 5.9 ta girgiza galibin jihohi dake gabar teku a gabashin Amurka.

Hukumar kula da al’amura karkashin kasa ta Amurka tace girgizar ta jiya talata ta auku ne a arewa maso yammacin birnin Richmond cikin jihar Virginia,kimanin kilomita 140 daga kudu maso yammacin birnin Washiongton.

Hukumomi sun bada umurni dukkan ma’aikata a majalisar dokokin Amurka, da ma’aikatar tsaro ta Pentagon, d a wasu hukumomin gwamnatin tarayya, har da helkwatar Muriyar Amurka duk su bar wuraren aikinsu.

Babu rahotanni nan take kan mutane da suka jikkata ko barna mai tsanani ba. Girgizar ta auku tsakanin karfe bakwai zuwa takwas agogon Najeriya, Nijar, d a kamaru, watau misalin karfe biyu zuwa uku na rana agogon Washington.

Har mazauna jihar Boston dake can arewaci, da tsibirin Martha’s Vineyard, a birnin Massachussetts, inda shugaba Obama yake hutu duk sai da suka ji motsinta.