Hukumar kula da lamura a karkashin kasa ta Amurka ta kiyasta karfin girgizar ya kai maki shida da digo biyu a sikelin, girgizar ta auku ne a wani wuri mai tazarar kilomita 10 gudu maso gabashin garin da ake kira Norcia. Anji motsin kasa a wurare msu nesa daga inda girgizar ta samo asali, har a babban birnin kasar Rome, mai tazarar kilomita 150 daga Norcia.
Girgizar ta auku ne da misalin karfe 3:30 na safe, sannan aka samu karin wasu kanana daga bisani. Wata hukumar tsaron kasar ta farin kaya tace daruruwan mutane sun jikkata, wasu masu yawa suna bukatar muhalli na wucin gadi.
"Girgizar kasa mai karfin gaske haka, kuma a inda ta auku galibi zata rusa gine gine, wanda zai janyo mace-mace," inji shugaban hukumar mai suna Fabrizio Curcio.