Girgizar Kasa Mai Karfi Ta Sake Aukuwa A Lombok Kasar Indonesia

Wani mai aikin ceto ya dauki hoton shugaban kasar daga baraguzen ginin wata makaranta

Jiya Lahadi girgizar kasamai karfin 6.9 ta sake aukawa tsibirin Lombok dake kasar Indonesia makonni biyu bayan wata da ta auku a yankin har ta yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 400

Hukumar lura da yanayin karkashin kasa ta Amurka tace, girgizar kasa mai karfin maki shidda da digo tara ta apku a tsibirin Lombok na kasar Indonesia jiya Lahadi, sa’o’i bayan aukuwar girgizar kasa mai karfin maki shidda da digo ukua tsibirin.

Haka kuma an bada rahoto hucin girgizar kasa har sau biyu a lokacin da girgizar ta auku.

Nan da nan ba’a samu rahoton ko wasu sun jikatta ba, to amma hukumar lura da bala’i ta kasar tace girgizar ta katse wutan lantarki a illahirin tsibirin. Tace gidaje da dama sun rushe a gundumar Sembalun a arewa maso gabashin tsibirin Lombok

Haka kuma anji duriyar girgizar kasar a tsibran Bali da Sumbawa da suke makwaptaka da tsibirin Lombok da kuma tsibirin Java (Yava) da Makassar a Sulawesi

Girgizar kasar ta jiya lahadi ta faru ne, makoni biyu bayan aukuwar wata girgizar kasa a tsibirin, har ta kashe fiye da mutane dari hudu.