Wata girgizar kasa mai karfin gaske ta wajajjaga tsibirin Crete na kasar Girka jiya Asabar.
Nan take dai babu wani rahoton game da wadanda abin ya rutsa da su ko kuma barnar da ta faru sanadiyyar wannan girgizar kasar da ta auku da yammacin jiya, wadda ta samo asali daga tekun Bahar Rum.
Cibiyar Nazarin Tekun Bahar Rum ta Turai ta ba da rahoton cewa girgizar kasar na da karfin shida a zurfin kilomita 10.
Ita kuma Cibiyar Nazarin Karkashin Kasa ta Amurka ta ce girgizar kasar ta nuna karfin 6.6 a zurfin kilomita 17; a yayin da ita kuma Cibiyar Nazarin Nayanayin Karkashin Kasa ta Kasar Jamus ke cewa gwajin farko ya nuna ta na da karfin 6.6.
Wannan girgizar kasar ta abka ma tsibirin a yayin kasar ta Girka ke kuma fuskantar yiwuwar fadawa cikin matsanaciyar karayar tattalin arziki yayin da ta ke fama da annobar cutar korona.