Gidauniyar Rochas Ta Kafa Shirin Ilmantar Da Matasan Najeriya Miliyan Guda

Sanata Rochas Okorocha

Gidauniyar Rochas yanzu ta kafa wani shirin da ake kira READ don ilmantar da kimanin matasan Najeriya marasa galihu miliyan guda kyauta.

Sanata Anayo Rochas Okorocha, tsohon gwamnan jihar Imo, wanda yanzu ke wakiltar gundumar Imo ta yamma a Majalisar Dattawa ta Najeriya shine shugaban gidauniyar, kuma ya yi cikakken bayani game da shirin a wannan hira da Muryar Amurka.

Wasu dai sun tofa albarkacin bakinsu da yaba wa kokarin gidauniyar Rochas wajen kirkiro shirin. Dakta Badamasi Burji, wani mai sharhi ne kan lamuran yau da kullum, wanda shi ma a kwana kwanan nan ya dauki nauyin ilmantar da yara 4,000 daga sassa daban-daban na jihar Kano.