Gidauniyar Dangote Ta Tallafawa Wadanda Rikicin Ile-Ife Ya Rutsa Da Su.

Hamshakin attajirin nan na Afirka Aliku Dangote.

Gidauniyar ta bada Naira milyan 50 ga Hausawa da Yarabawa wadanda rikicin Ya janyowa hasara iri daban daban.

Gidauniyar Dangote ta bada tallafin Naira milyan 50 ga Hausawa da Yarabawa, wadanda rikicin kabilanci tsakanin sassan biyu ya rutsa da su a watanni baya a Sabo Ile-Ife.

Mai martaba sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi na biyu, wanda ya halarci bikin mika gudumawar a fadar mai martaba Oni na Ife, yayi kira ga ‘yan Nijeriya su zauna lafiya da juna. Sarki Sanusi, yaci gaba da cewa zaman lafiya shine tushen arziki.

Sarki Sanusi, yace Allah yayi mu kabilu daban daban da addinai daban daban don mu zauna lafiya.

Sarki Sanusi, ya yabawa Oni na Ife, kan irin rawar da ya taka wajen kashe wutar rikicin. Yace sarkin bai nuna banbanci tsakanin Yarabawa da Hausawa ba, yasa aka kama duk wadanda suke da hannu a rikicin.

Wata hadimar Aliku Dangoten, Zuwaira Yusuf, wacce ta mika check na kudin tace, duka duka mutane 220 da ashirin ne suka tafka hasara iri daban daban, daga gine gine da kayan sana’o’insu. A cikinsu akwai Hausawa ko ‘yan Arewa 78, wadanda suka sami Naira milyan 35, yayinda mutum dari kuma Yarabawa wadanda suka sami Naira milyan 15 a zaman diyya ko tallafi kan irin barna da aka yi musu lokacin rikicin.

Wadanda suka amfana daga wannan tallafi sun bayyana farin cikinsu, lokacinda suka tattauna da wakilin Sashen Hausa Hassan Umaru Tambuwal.

Your browser doesn’t support HTML5

Gidauniyar Dangote ta tallafawa yarabawa da hausawa a ile ife