Gidauniyar Bill da Melinda Gates Zata Taimakawa Jihar Neja kan Bunkusa Harkokin Kiwon Lafiya

Alhaji Abubakar Sani Bello, gwamnan jihar Neja

Gidauniyar Bill da Melinda Gates zata taimakawa jihar Neja wajen horas da ma’aikatan kiwon lafiya wadanda zasu dinga aiki a kananan assibitoci dake cikin karkara domin bunkasa harkokin kiwon lafiya a jihar

Gidauniyar Bill da Melinda Gates ta kasar Amurka zata taimakawa jihar Neja kan bunkasa kiwon lafiya a jihar a matakin farko.

Gidauniyar zata horas da jami’an kiwon lafiya da zasu dinga aiki a assibitocin yankunan karkara.

Shugaban Gidauniyar, Dr Chris Elias, ya jadadda muhimmancin maida hankali akan kiyon lafiyar al’umma a koda yaushe, kuma wannan shine aka fi baiwa mahimmanci a yarjejeniyar tasu da gwamnatin jihar Neja.

A karin hasken da ya bada, Gwamnan jihar, Abubakar Sani Bello, yace da farko zasu horas da ma’aikatan kananan asibitoci. Yace a shekarar farko gwamnatin jihar zata biya kashi ishirin na kudin horas da ma’aikatan, gidauniyar kuma ta biya sauran kashi tamanin, yayinda a shekara ta biyu jihar zata biya kashi talatin. Gwamnan yace haka zasu dinga yi har komi ya dawo hannun gwamnatin.

Daga karshe tawagar gidauniyar da ta gwamnan jihar da ta ministan kiwon lafiyar Najeriya, Farfesa Isaac Adewale, sun isa kauyen Fuka inda aka samu bullar cutar zazzabin masassharar Lassa a kwanakin baya domin bude wani asibitin da gwamnatin tarayya ta gina.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Gidauniyar Bill da Melinda Gates Zata Taimakawa Jihar Neja kan Bunkusa Harkokin Kiwon Lafiya - 2' 54"