Bayan da aka sako Sanata Dino Melaye wanda aka tsareshi yau litinin a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe yayin da zai je Morocco, 'yan sanda sun yi wa gidansa a Abuja kawanya.
"'Rundunar kwantar da tarzoma sama da 30 dauke da makamai sun yi wa gidana a Maitama Abuja diran mikiya. Sannan duk hanyoyin zuwa gidana an rufe ba shiga-ba-fita " inji Dino Melaye a shafinsa na twitter.
Haka kuma ya wallafa cewa, 'yan sandar sun cafke dan uwansa da abokinsa a gaban gidansa din.
Kawo yanzu rundunar 'yan sanda ba su ce komai dangane da abun da ke faruwa ba.
A baya dai 'Yan Sanda na zargin Melaye da kin bayyana a gaban kotu don fuskantar shari'a, a bisa zargin da ake masa na daukar nauyin wasu bata-gari da mallakar makamai ba bisa ka'ida ba.