Shugaban hukumar kwallon kafa ta Duniya ta FIFA Gianni Infantino ya aike da sakon ta’aziyarsa ga iyalan Chief Taiwo Ugunjobi, tsohon babban sakataren tsohuwar hukumar kwallon kafar Najeriya ta NFA wanda ya rasu a ranar Litinin.
A wata wasika a ranar Talata 19 ga watan Faburairu 2019, zuwa ga shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya, Mr Amanju Melvin Pinnick, jagoran kwallon kafa na duniya ya ce yana bayyana alhinin sa a wannan babban rashi na mutuwar tsohon dan wasan kasa da kasa na Najeriya, shugaba a harkar kwallon kafa, wanda ya taka rawar gani a fannin wasan kwallon kafa a Najeriya da Afrika da ma duniya baki daya.
Sakon na Gianni Infantino yana cikin sakwannin masoya da abokan arzikin marigayin da suka kwarara daga sassa da dama na duniya, suna taya al’ummar Najeriya da iyalan marigayi Chief Taiwo bakin cikin mutuwar sa.
Taiwo ya yi abin a zo a gani a fannin kwallon kafa. Masu sha’awar kwallon kafa ba zasu manta matsayin sa na keftin ‘yan wasan Shooting Stars SC da suka kai wasan karshen a gasar cin kofin kungiyoyin Afrika a shekarar 1984. Bayan ya yi ritaya a wasa, ya rike mukamin babban sakataren tsohuwar hukumar kwallon kafa ta Najeriya ta NFA tsakanin shekarun 2002 da 2005, ya kuma taba zama mamban hukumar ta yanzu ta NFF tsakanin shekarun 2006 da 2010.
Marigayin ya kuma jagoranci wasanni biyu a gasar cin kofin duniya a shekarar 2010 a matsayin babban jami’i, yana kuma cikin tawagar hukumar kwallon kafa ta Najeriya a gasar cin kofin duniya a shekarun 2002 da 2010. Shugaban hukumar FIFA ya ce lallai duniya ba zata manta da gudunmuwar Chief Taiwo Ogunjobi ba.