Gianluigi Buffon: Zai Koma Tsohuwar Kungiyarsa Ta Juventus

Dan wasa Gianluigi Buffon

Tsohon mai tsaron raga na kasar Italiya Gianluigi Buffon ya amince da ya sake komawa tsohuwar kungiyar sa ta Juventus, bayan shafe kakar wasa daya kacal a kungiyar kwallon kafa ta Paris St-Germain dake Faransa.

Buffon ya koma PSG, daga Juventus a ranar 19 ga watan Mayu shekara ta 2018, inda ya buga mata wasanni 25 a tsawon zamansa da yayi na shekara guda.

Dan wasan mai shekaru 41, da haihuwa kafin ya bar Juventus zuwa PSG, a 2018 sai dai ya shafe shekaru 17 a Juventus yana buga mata wasanni inda yanzu ya koma.

Mai tsaron ragar, ya kafa tarihin zama dan wasan da yafi wakiltar kasarsa Italiya, inda ya buga mata wasanni har 176, ciki harda gasar cin kofin duniya da ya lashe a 2006.

Bayan haka Buffon ya lashe gasar Serie A, na kasar Itali sau tara da Coppa Italia sau hudu.

Haka kuma a komawarsa PSG ya lashe gasar Lig ta Faransa a kakar da ta gabata. Buffon zai zamo dan wasa na uku da Juventus ta dauka kyauta a bana, bayan da ta dauki Adrien Rabiot shima daga PSG da kuma Aaron Ramsey daga Arsenal.