GHANA: Zaben Kananan Hukumomi

Shugaban Ghana John Dramani Mahama.

Yau ake zaben kananan hukumomi a kasar Ghana amma saboda wasu kurakurai hukumar zaben ta dakatar da na wasu wurare.

A wata mazaba a jihar Ashanti hukumar zabe ta dage zaben na yau saboda wasu kurakurai da ta gano wurin buga takardun zaben.

Hukumar ta yi alkawarin buga wasu takardun kana ta shirya zaben wannan yankin a wani lokaci nan gaba. Alamarin dai ya tada hayaniya inda wasu suka soma maganganu. Wasu sun yi korafin cewa basu san dalilin da ya sa aka daga zaben ba.

Amma wani jami'in zabe yace saboda yawan 'yan takara wasu sunayensu basu shiga cikin takardar zabe ba. Saboda haka wajibi ne su tsayar da zaben domin su samu su kara sunayen da babu su yanzu. Wani jami'in yace basu ma buga takardun zaben ba.

Mutane sun mamaye ofishin zaben dake yankinsu har sai da 'yansanda suka tarwatsasu. Jami'in 'yansanda yace tunda hukumar tace ba zata gudanar da zabe yau dole ne su tabbatar da tsaro jama'a kuma su jira ranar zaben.

Kazalika a mazabar Kasafuredu dake garin Sekondi a jihar yammacin kasar dan takarar kuma wakilin mazabar mai ci yanzu Nana Igye mabiyansa sun tada tarzoma tare da yin zanga zanga. Sun yi kone-konen tayoyi da lalata kaddarori tare da kai hari akan duk wanda ya fito da niyyar jefa kuri'a.

A wasu yankunan arewacin kasar kuwa ruwa da aka yi kamar da bakin kwarya ya yi sanadiyar jinkirin da aka samu a yankin. Ruwan sama ya yaye rumfunan zabe dake karkashin bishiyoyi. Naurorin tantance masu zaben kuma suka jike.

A wani yankin kuma takardun zaben ne suka jike saboda ruwan sama. An samu jinkiri har ma wasu masu kada kuri'a suka koma gidajensu.

To saida a babban birnin kasar, Accra mutane na daridari da zaben. Yawanci basu fito ba.

Ga rahoton Yakubu Baba Makeri.

Your browser doesn’t support HTML5

GHANA: Zaben Kananan Hukumomi