GHANA: Yau Take Ranar Bikin Harshen Uwa Ta Duniya

Ranar Harshen Uwa Ta Duniya

A shekarar 2000 aka kebe ranar 21 ga Fabrairu, a matsayin ranar bukin harshen uwa ta duniya (IMLD).

Hakan ya samo asali ne daga ranar 17 ga watan Nuwamba 1999, inda Hukumar Raya Ilmi, Kimiyya da Al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya, UNESCO, ta sanar da ita a matsayin rana ta musamman domin bunkasa harsunan duniya da raya al'adu a tsakanin al'umma.

Daga bisani kuma Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ita a hukumance.

Muhammad Bashiru Shehu, wanda aka fi sani da Sir Bash, manazarci a harkar ilimi ya yi karin bayani a kan wannan rana ta bukin harshen uwa ta duniya ta 2023.

Ya ce, hukumar UNESCO ta yi nazarin cewa, ilmantar da yara cikin harshen su zai kara musu fahimta. Ta kara da cewa Ghana ta yi bincike a shekarar 2006 inda ta gano cewa, kashi 26 cikin 100 na yaran da suka kammala Firamare ne kawai suke iya karatu kadan.

Ranar Harshen Uwa Ta Duniya

Taken bukin Ranar Harshen Uwa ta Duniya na shekarar 2023 shi ne, “Ilmantarwa da mabanbantan harsuna - zai canja fasalin ilimi”. Kididdigar hukumar UNESCO na cewa, kashi 40 cikin 100 na al'ummar kasashen duniya ba su samun ilimi a cikin harshensu na asali ko wanda suke fahimta ba.

Haka kuma binciken da hukumar ta yi ke cewa, kashi 30 cikin 100 na yaran da ake koyar da su cikin harshen uwa zuwa karshen ilmin firamare suna fahimta fiye da wadanda ba sa jin yaren koyarwar.

Dokta Nasiba Tahir, Malamar ilmin sanin halayyar dan adam, a jami’ar Islamiya dake Accra ta bayyana muhimmancin koyarwa da harshen uwa ga ‘yan makaranta.

Ta ce, yana karawa yaro karsashi zuwa makaranta domin ana koyar da shi da yaren da yake tunani da shi kuma yafi fahimta.

Ghana kasa ce da take da harsuna da yawa, shin ko da wane harshe za a koyawa yara da suke da mabanbantan yare a cikin aji? Muhammad Bashiru Shehu ya ce, sai a dauki harshen Twi (Asante) da yafi rinjaye a kudancin Ghana, sai kuma a yi amfani da Dagombanci (Dagbani) ko Hausa ko wani yare da yafi rinjaye a arewacin Ghana.

Har wa yau dai, a wannan rana ta harshen uwa, hukumar UNESCO na tunatar da duniya mahimmancin kiyaye harsunan asali.

Saurari rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

IMLD.MP3