A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar da sa hannun mataimakin Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Fice ta Ghana, Laud Ofori Affrifah, hukumar tace mai yiwuwa 'yan Boko Haram da suka tsere daga gidan yarin Kuje, za su yi yunkurin yin hijira zuwa Ghana ta hanyoyin da aka amince da su da kuma haramtattun hanyoyi, idan aka yi "la'akari da yanayin kaura da 'yan Najeriya ke yi zuwa wannan yankin."
Sanarwar tace, "a daren Larabar 6 ga watan Yuli, wasu da ake zargin ‘yan Boko Haram ne, suka fasa gidan yarin Kuje dake Abuja, inda rahotannin hukuma suka nuna cewa, akalla fursunoni 443 cikin 879 ne suka tsere sakamakon fasa gidan yarin. Daga cikinsu, akwai akalla fursunoni 64 da suke da alaka da kungiyar Boko Haram."
Domin haka hukumar shige da fice na Ghana na sanar da duk kwamandojin shiyyoyi da su dauki tsauraran matakai a duk iyakokin shiga don dakile tare da kame duk fursunonin da za su yi yunkurin kutsawa cikin kasar nan.
A hirar shi da Muryar Amurka, masani a kan harkokin tsaro, Adib Sani, ya ce, ya dace da wannan matakin da hukuomin Ghana ta dauka. Yace, Ghana ce kasa ta farko da za su nemi mafaka sabili da matsayin ci gabanta a yanzu da kuma kasancewarta ana magana da harshen Ingilishi.
Adib Sani ya shawarci hukumomin Ghana da su wayar da kan mazauna iyakokin kasar cewa su kiyaye kuma su sa ido a kan masu shige da fice, kuma masu gidajen haya su binciki duk wadanda suka zo neman hayan gida kafin su ba su.
A ranar 19 ga watar Afrilu 2019, hukumar ‘yan sandan Ghana reshen gundumar Ada da ke yankin Volta, ta kama fursunoni 9 da suka tsere daga gidan yarin Owerri, yayin da suka yi kokarin shigowa kasar ta Kogin Volta.
Saurari cikakken rahoton Idris Abdullah Bako cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5