Bikin da shugaban kasar na yanzu John Dramani Mahamma ya halarta ya fara da faifan murya Kwame Nkurma, shugaban kasar na farko wanda ya gargadi 'yan kasar da su so kasarsu, su rungumeta da kunar gasken gaske.
Kwame Nkurma a wancan lokacin yace kishin kasa shi zai taimakawa kasashen Afirka su yi gogayya da cudanya da sauran kasashen duniya.
A wurin paretin bikin zagayowar ranar samun 'yancin Ghana wadda ta cika shekaru 59 da samun 'yanci jiya Lahadi a birnin Accra shugaban kasar na yanzu John Dramani Mahamma ya maimaita kiran na kishin kasa. Tace zamu iya samun sabanin ra'ayi amma bai hanamu yin alfahari da son kasarmu ba. Duk da haka 'yan Ghana su san al'umma daya suke, waato tamkar tsintsiya madaurinki daya.
Muryar Amurka ta tambayi Malam Bawa Abubakar ko yanzu mutane na kishin kasar Ghana kamar da can sai yace a gaskiya 'yan Ghana basa son yaki a kasarsu. Abubuwa da dama suna faruwa a kasar da zasu iya kaiga yaki a wasu kasashen. Mutane sai su ce a yi hakuri a zauna lafiya. Yace wannan wata hanya ce ta nuna kishin kasa.
Dangane da sauran kasashen Afirka inda aka dinga samun rigingimu Malam Bawa Abubakar yace laifin gwamnatocinsu ne. Wasu alkawuran da suka yiwa jama'a basu cikasu ba. Sau tari jama zasu tashi babu wuta, babu ruwan sha babu hanyoyin sufuri kan lafiyayyun tituna. Gwamnatoci yanzu basa cika alkawari.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5