Yayin zantawarta da muryar Amurka Rafiya Musah shugabar sashen kulada masu fama da cutar a'asibitin Adabraka PolyClinic dake Accra babban binin kasar Ghana tace masu luwadi madigo da mata masu juna biyu, tare da masu sana'ar karuwanci ke kan gaba cikin jerin wadanda suka harbu da cutar abaya bayannan.
Sai dai a nasa bayanin, mai magana da yawun matsugunin masu luwadi da madigo a Ghana wato LGBTQI da dangoginsu Abdul Wadud Muhammad ya nuna rashin gamsuwa da jawabin hukumar inda yake cewa masu luwadi a Ghana suna isa a gwada su amma mafi yawan alumman kasar basu yin hakan.
Ya kara da cewa, "in aka ce cutar tafi kama masu luwadi da dangoginsu ba gaskiya bane. Abinda ya kamata mu sani shine mu da muke luwadi a Ghana tare da mata masu juna biyu ne ake gwada mu sosai amma in ana so a san masu yawan kamuwa da cuta to kamata yayi da gwamnati ta fadada gwaje gwajenta a lokacin zata gano masu yawan kamuwa da cutar."
Matsugunan Musulmi na daga cikin wuraren da cutar tafi yaduwa a baya bayannan abinda hukumomi ke bukatar da masu aure fiye da daya su rika gwaji kafin su yi aure.
Dangane da haka, Sarkin Addini ajahar Ashanti na Ghana Dawood Akanni ya bukaci da an ga aluma a rika isa ana gwaji musamman wadanda ke da niyan kara mata tare da daukan matakan kariya domin ganin an dakile yaduwar cutar,
Gwamnati dai ta sanar da daukan matakai ciki har da wasu 245,000 masu fama da cutar da suke samun magani amma babban kalubalenta a yanzu shine anfi maida hankali akan cutar Covid 19 da Marburg.
Saurari cikakken rahoton Hamza Adams cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5