Ghana Na Shirin Raba Rana Da Kamaru A Gasar Afrika Na U-23 - Tanko

Ibrahim Tanko, Mai Horar da 'yan wasan Ghana

Mai horar da ‘yan wasan Ghana ‘yan kasa da shekaru 23 Ibrahim Tanko, yace ‘yan wasansa sun shirya su fafata da ‘yan Kamaru a wasan farko na zakarun Afrika ‘yan kasa da shekaru 23.

Ghana U23 Coach Ibrahim Tanko insists his side is battle ready ahead of the U-23 Africa Cup of Nations

A gobe Juma’a ne dai ‘yan wasan Black Meteors ta Ghana zasu raba rana da Indomitable Lions ta Kamaru a filin wasa na International a birnin Alkahira, bayan haka Ghana zata kara da Misra mai masaukin baki da kuma kasar Mali a ranakun 11 da 14 na watan Nuwamba.

Wannan ne karon farko da Ghana ke shiga wannan gasar ta zakarun Afrika kasa da shekaru 23, ta kuma lashi takobi cewa zata kai ga wasannin karshe, lamarin da zai bata cancantar shiga gasar ta duniya na shekarar 2020 da za a yi a birnin Tokyo na Japan.

Tanko yace yana kyautata zaton ‘yan wasan sun kimtsa su lashe wasan na gobe Juma’a da zasu yi da Kamaru da ma wasanni na gaba. ‘Yan wasan sun himmantu su taka leda su yi nasar domin kasa tayi alfahri dasu.

Ina sa ran idan ‘yan wasan suka ci gaba da haka har gobe Juma’a wasan su zai yi kyau. Yace sun san wasan dake a gaban su gobe Juma’a kana yace sun shirywa wasan, inji Ibrahim Tanko a lokacin tirenin a birnin Alkahira.