Kasar Ghana a yau ta cika shekaru 67 da samun ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka.
ACCRA, GHANA - Kasar ta sami 'yancin kanta bayan shekaru 83 na mulkin mallaka na Birtaniyya, kuma ta kasance kasa ta farko da ta samu 'yancin kai daga yankin Kudu da Saharar Afirka.
Taken bukin wannan shekarar, "Dimokradiyyarmu, Alfaharinmu", ta mayar da hankali ne wajen karfafa dabi'un dimokradiyya da kuma samar da zaman lafiya, musamman ganin zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki na 2024 mai zuwa.
Shugaban kasar Ivory Coast, Alhassan Ouattara, ne babban bakon bukin.