GHANA: Mahajjata 3069 Kawai Ne Za Su Samu Zuwa Aikin Hajji Bana

HAJJ

Bayan kwashe shekaru biyu ba a gudanar da aikin hajji ba a fadin duniya, sanadiyyar annobar Korona, an sake bayar da dama, amma ba kamar yadda ya ke a baya ba.

A Ghana Mahajjata 3069 kawai ne za su samu zuwa aikin Hajji bana; kuma har yanzu hukumomin aikin hajji a Ghana basu fitar kudin hajj ba

Bayan kwashe shekaru biyu ba a gudanar da aikin hajji ba a fadin duniya, sanadiyyar annobar da ta addabe duniyar, Saudiya tabce zata ba wa mutum miliyan daya daga wajen kasar damar aikin hajji a bana, daga ciki kuwa kasar Ghana ta samu Kujeru 3069.

Alhaji Garba Albalad, daya daga masu jigilar mahajjata a Ghana, ya ce shi kadai ya kan yi jigilar mutum dubu daya kowace shekara, kuma akwai kudin mahajja 2000 wadanda suka biya kudin hajjinsu shekara biyu da ba a tafi hajji ba,

Alhaji Papa Angola, mai bibiyar aikin hajji tun ba yau ba, afadarsa hukumar aikin hajji ta cika alkawarin da ta dauka cewa ba za ta kara kudin hajji ga wadanda dama kudinsu ke hannunta ba.

Alhaji Abubakar Sidiq Daraktan Sadarwa daga hukumar aikin hajji ya ce bana hajji zai yi tsada saboda wasu gyare-gyaren da karin kudin haraji daga kasar saudiyya.

Saurari cikakken rahoton Hauwa Abdulkarim:

Your browser doesn’t support HTML5

3069 GHANA HAJJ 2022.