A cewarsa, Ghana ta samu wannan nasara ne bayan da ta tura dakarunta a baya-bayan nan don taimakawa wajen wanzar da zaman lafiya a Sudan.
Daya daga sojojin da aka aika wajen wanzar da zaman lafiya Kaftin Shamsudeen Salifu kuma Limamin sojoji a Ghana ya ce tun shekarar 1960 kasar Ghana ta fara zuwa wajen wanzar da zaman lafiya.
A cewarsa kuma su kan iya kai shekara ko fiye da haka sanna majalisar dinkin duniya ta basu damar zuwa gida dan hutu.
Masanin harkokin tsaro Mallam Irbad Ibrahim ya ce kasar Ghana ce kasa ta goma acikin kasashe 200 a duniya da ta samu wannan yabo.
Ya ce baya ga kasar Sudan akwai wasu kasashe da Ghana ta aika sojojin kamar kasar DR Congo, Lebanon, Mali, da dai sauransu.
Ya bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta bada duk gudumuwar da tace wajen magunguna da makamai.
Saurari rahoto cikin sauti daga Hawa AbdulKarim:
Your browser doesn’t support HTML5