Kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles na tarayyar Najeriya Gernot Rohr, ya gayyaci dan wasan gefe na kungiyar CSKA Sofia dake kasar Bulgaria, mai suna Efosa Solomon Otabor, cikin tawagar 'yan wasan da zasu fafata a wasan sada zumunci da kasar Brazil a ranar 13 ga watan Oktoban 2019 a Kallangin.
Hukumar Kwallon kafar ta Najeriya ta wallafa a shafinta na sada zumunta cewar, dan wasan Efosa zai maye gurbin takwaransa Samuel Kalu wanda yake fama da jinya.
Samuel Kalu yana cikin tawagar Super Eagles amman ya samu rauni a yayin da yake atisaye a kulob dinsa Bordeaux na kasar Faransa, a ranar Asabar da ta gabata.
Dan wasan Solomon Otabor mai shekaru 23 da haihuwa, ya buga wasanni bakwai wa kungiyarsa ta CSKA Sofia, cikin gasar lig na kasar Belgium a wannan kakar wasan bana.
In ba a mantaba kwannan nan ne Rohr ya bayyana sunan Tyronne Ebuehi, a matsayin wanda ya maye gurbin dan wasan baya na Legenes Kenneth Omeruo.