Shugaban kasar Laberiya, George Weah, ya ce kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Super Eagles, tana da damar lashe gasar cin kofin duniya da za'ayi a kasar Rasha a watan Yuni shekara 2018 idan an yi abubuwan da ya dace wa tawagar ‘yan wasan.
Shugaban ya fadi haka ne a wata ganawar Sirri da sukayi da Shugaban Najeriya Muhammad Buhari a fadan Gwamnati dake Villa dake babban birnin tarayya Abuja ranar Litinin.
Mr. Weah ya ce ya kamata "duk abin da 'yan wasan ke bukata to ya zamo dole ne a Samar dasu a muhallinsu kafin gasar cin kofin duniya". Wannan ita ceshawarar da Nijeriya ya kamata ta bi don tabbatar da shirye-shiryenta na samun nasara a gasar.
Ya bayyan cewa yayin da suke buga wasa a Turai, "suna zuwa sansanin wasa kuma ana ba da dukkan abinda ya dace kuma su ke bukata, ya kara da cewa ba sa yin komai sai dai dan shakatawa da kuma wasa, ba a yarda dan wasa ya damu da sauran abubuwa ".
A kwananne Shugaban hukumar kula da kwallon Kafa ta tarayyar Najeriya, Amaju Pininick, ya bayyana cewar Najeriya zata kashe dalar Amurka miliyan $2.8 wajan gasar cin kofin duniya da za'ayi a kasar Rasha inda yace baya so a samu wata matsala daga bangaren hukumar NFF akan batun gasar.
Your browser doesn’t support HTML5