Wani masani akan kudin tsarin mulkin Nigeria Barrista Isiyaku Baru ya ce a sashe na 66 na kudin tsarin mulkin ya ambaci mutanen da ba za su iya tsayawa takarar neman mukamin siyasa ba a kasar. Ya ce duk mutumin da aka daure shi a gidan yari na ba zai iya tsayawa takara ba.
Kwamishinan zabe na jihar Pilato Alhaji Hussaini Halilu Pai ya shaida wa Sashen Hausa cewa ba su ke zaben dan takara ba, ya ce duk wanda jam’iyya ta ce shine dan takara toh hukumar zabe ba za ta ja da ita ba kuma dole ne su amince shi.
Amma Jam’iyyar APC a Nigeria ta ce ba ta da masaniyar cewa Joshua Dariye ya sayi fom din tsayawa takarar neman sanata, a cewar mataimakin ma’ajin jam’iyyar Barrista Muhammad Tanko Zakari, inda yake cewa su a jam’iyyance ba su wake san gidan yari ba da wanda ba ya gidan yari. Ya ce su dai sun sayar da fom kuma duk wanda dan jam’iyya ne, kuma yana da sha’awar fitowa takara za su saida masa fom.
Your browser doesn’t support HTML5