Kocin Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona Ernesto Valverde, ya nuna rashin jindadinsa da kasancewar dan wasansa Lionel Messi, shine na biyar acikin jerin wadanda aka zaba a gwarzon 'yan wasan duniya 2018.
Kocin yace sam ba'a yi adalciba kan wannan zaben ba, ganin yadda dan wasan Messi ya samu nasarrori, inda ya kasance dan wasan da yafi yawan zurara kwallaye a raga a turai har guda 34.
Haka kuma ya taimaka wa Barcelona ta lashe gasar Laliga na kasar Spain da kuma Copa del Rey, a shekarar.
Ernesto Valverde, yace duk da irin nasarorin da dan wasan Messi ya samu, amma maki 280 kacal ya samu a zaben da akayi na gwarzon dan wasa na bana a mataki na biyar.
Luka Modric wanda ya lashe zaben ya samu maki 753, Cristiano Ronaldo yazo na biyu da maki 476, Antoine Griezmann maki 414, matashin dan wasan Faransa na kungiyar Paris-saint Germain, Kylian Mbappe a matsayi na hudu da maki 347.
Sai dai duk da wannan korafi na kocin Barcelona a gefe guda ya taya Luka Modric wanda ya lashe kyautar a bana murna.