A cigaba da gasar cin kofin nahiyar kasashen Afrika dake gudana a kasar Masar, na shekarar 2019. Bayan kammala wasannin rukuni, kungiyoyi 8 ne yanzu haka za su kama hanyar dawowa gida, yayinda 16 za su fafata, a zagaye na biyu da zai baiwa kungiyoyi 8 damar samun tikiti zuwa wasan na kusa da na daf da karshe Quarter final.
Yanzu haka an fidda Jadawalin wasannin na kasashe 16 da zasu fafata inda a ranar Juma’a 5 ga watan Yuli shekara 2019 za'a fara tsakanin kasar Uganda da Senegal.
Morocco da Benin kowa zasu kece raini ne ranar Asabar 6 ga watan Yuli sai kuma Najeriya da kasar Kamaru. Ranar Lahadi 7 ga watan Yuli masu masaukin baki Masar da Afrika ta kudu.
Madagascar da Demokkuradiyar Congo, sauran wasannin kuwa Algeriya na tare da kasar Guinee, ranar Litinin 8 ga watan Yuli 2019 Ghana da Tunisia,
sai kuma kasar Mali da Cote D’Ivoire.
Wadannan sune kasashe 16 da zasu gwabza domin neman zuwa mataki na gaba, cikin gasar ta cin kofin Afrika na shekara 2019 wanda kasar Masar ta karbi bakoncin sa.