Sabuwar tashar Hausa ta VOA da ake kamawa a wayoyin salula ko kwamfutar hannu, DandalinVOA.
WASHINGTON, DC —
Sabuwar tashar Hausa ta VOA da ake kamawa a wayoyin salula ko kwamfutar hannu, DandalinVOA, na gayyatarku da ku saurare mu daga karfe 5 zuwa karfe 6 na yamma agogon Najeriya, a wannan makon, a lokacin da muke gabatar da wakokin Indiya. A tsakiyar wakokin na Indiya, zamu sanya wata wakar gargajiya ta Hausa. Muna son ku rubuto ku fada mana sunan wakar da wanda ya rera ta.
Zamu bayar da kyautar riguna guda 10 na DandalinVOA ga mata biyar da maza biyar da suka amsa wannan tambaya daidai. Idan wadanda suka amsa tambayar daidai sun fi yawan kyaututtukan da za a bayar, to zamu gayyato wani ko wata daga wajen sashen Hausa domin su zo su zabo maza biyar da mata biyar daga cikin wadanda suka amsa tambayar daidai.
Za a rufe wannan gasa a ranar lahadi, 20 Afrilu, 2014 da karfe 12 na dare agogon Najeriya.
Zamu rubuta sunayen wadanda suka yi nasa a wannan shafin, zamu kuma sanar a cikin shirye-shiryen DandalinVOA a ranar litinin, 21 Afrilu, 2014.
A aiko da amsar zuwa ga: Hausa-Service@voanews.com
Allah Ya ba da mai rabo sa’a, kuma a ci gaba da sauraron DandalinVOA, dare da rana, a wayoyinku na salula.