Kasar Netherlands ta samu kaiwa matakin ‘Kwata-fainal’ a Gasar Cin Kofin Duniya ta bana da ke gudana a kasar Qatar, bayan da a yau Asabar ta doke Amurka da ci 3-1 a wasan zagaye na biyu a gasar.
A yau Asabar ne dai aka soma fafatawar ta ‘yan zagaye na 16 a gasar, bayan kammala matakin rukuni a jiya Jumma’a, wanda ya fitar da kasashe 16 da su ka zo na daya da na biyu a kowane rukuni da za su fafata a zagayen na biyu.
Ko bayan wasan na Amurka da Netherlands a yau, Argentina da Australia ma na fafatawa a yau. A sauran wasannin zagayen kuma Faransa da Poland za su kece raini; Ingila kuma ta kara da Senegal; Japan da Croatia; Brazil da Koriya Ta Kudu; Morocco da Spain, yayin da Portugal kuma za ta buga da Switzerland.
Manazarta harkokin wasanni na ci gaba da sharhi kan kwazo ko akasin haka na kasashen nahiyar Afurka a gasar ta cin kofin duniya ta bana a Qatar. Kasashen biyar ne dai ke wakiltar nahiyar ta Afurka a gasar. Kuma tuni aka yi waje rod da kasashe uku da su ka hada da Ghana da Tunisiya da Kamaru a matakin rukuni, yayin da kasashe biyu, wato Morocco da Senegal kuma su ka samu tsallakewa zuwa mataki na gaba a gasar.
To ko yaya manazarta ke ganin wakilcin na nahiyar Afurka? Umar Faruk Bukkuyum dan jarida kuma mai fashin baki kan harkokin wasannin kwallon kafa ya ce: “Za a iya cewa kasashen Afurka da su ka wakilci Afurka a wannan gasar sun taka rawa, amma rawar dai ba ta kai yadda ake bukata saboda kasashe biyar da su ka wakilci Afurka, wadanda yanzu an cire uku saura biyu – irinsu Ghana, Tunisiya, Kamaru da dai sauransu – za a iya cewa, a hakikanin gaskiya, rawar da su ka taka ba ta taka kara ta karya ba domin irin zaratan ‘yan wasan da Ghana ke da su, idan mu ka kalli yadda ta cire Najeriya a Abuja, da kuma yadda ita ma Kamaru ke da zaratan ‘yan wasa, ya kamata a ce sun je zagaye na biyu – zagayen bugun daga shi sai a dawo gida, saboda nan ne ake gwada kwanci a irin karfin da mutum ke da shi. Amma gaskiyar magana wannan fitar da su ka yi a zagaye na farko – gaskiyar magaba basu taka rawar gani ba, babu wani abin armashi da da za mu iya cewa mun gani, da su ka yi, saboda ai dukansu sun a taka leda a kasashen Turai, ba wai kananan ‘yan wasa ba ne”
Da yake amsa tambaya kan tasirin da ya ke ganin kasashen Afurka biyu da su ka samu tsallewa za su iya yi a gasar nan gaba, sai ya ce, “Kasashen biyu na Afurka da su ka rage: ma’ana Senegal da Morocco, idan ana duba ko wace ce ake tunanin za ta iya kaiwa gaba, ma’ana za ta iya cin wannan zagayen, kasar Morocco ce a hakikanin gaskiya saboda kasar ta Morocco, abin da ta nuna a wasannin guda uku da ta buga, ta zo ta ci wannan kofin ne, ba wargi ta zo yi ba; saboda karfin da ‘yan wasan su ka nuna a gaba da kuma yadda su ka rike tsakiya da kuma yadda su ke da ‘yan baya – wanda ainihin sun nuna a wasanninsu uku da su ka yi – ina ganin Morocco na iya cin wannan kofin, don saboda – su waye masu karfin da su ka rage? Kasashen Ingila ne da Spain da kuma Faransa. Dukkansu babu kasar da Moroco ke tsoro cikinsu.”
Saurari cikakken rahoton Murtala Sanyinna:
Your browser doesn’t support HTML5