Tawagar Super Eagles ta Najeriya ta doke Kamaru da ci biyu da nema a wasan zagaye na biyu na gasar cin kofin nahiyar Afirka ga suka buga a ranar Asabar.
Ademola Lookman mai buga wa kungiyar kwallon kafa ta Atalanta a kasar Italiya ne ya zura wa Najeriya kwallaye biyu. Daya kafin a tafi hutun rabin lokaci na biyu bayan an dawo hutu a misali minti 90 na wasan da ake bugawa a kasar Kwaddebuwa.
Hakan na nufin Kamaru ta fita da gasar kuma Najeriya za ta fafata da Angola, wadda ta fitar da Namibiya, a dayan wasan da aka buga a ranar Asabar.
A dayan wasan kuma, dan wasan Angola, Gelson Dala ne ya zura kwallaye - biyu kafin a tafi hutun rabin lokaci.
Da aka dawo kuma Agostinho Mabululu ya zura kwallo ta uku.
Wasan ya yi zafin da sai da alkalin wasa ya ba kowane bangaren jan kati - abin da ya sa dukkan su suka buga wasan da 'yan kwallo goma-goma.
Mabululu ya kafa tarihi a Angola na zama dan wasan kasar na farko da ya taba cin kwallaye uku a gasar kofin nahiyar Afirka.