Kungiyar Fulani makiyaya Miyetti Allah a Najeriya, ta koka kan abunda ta kira ta'azzarar ci gaba da garkuwa da 'yayan kungiyar, musamman a jihohin Nija, da Kogi da kuma wani bangare na birnin tarayya Abuja.
Da yake magana kan wannan batu mataimakin shugaban kungiyar ta kasa, Alhaji Husseini Bosso,yace matasalar tana kara tsanani duk da cewa jami'an tsaro suna bakin kokarinsu.
Alhaji Husseini Bosso, yace ahalin yanzu akwai 'yan kungiyar kamar tara da barayin suke ci gaba da garkuwa das su a sassan Najeriya daban daban cikin dazuzzuka. Yace duk da haka wasu sarakuna kamar na Lapai, sun tashi haikan wajen jawo kan matasa-Fulani wadanda ake yawan zargi da sace-sacen da kuma garkuwa da mutane.
A Jihar Nija, wani makiyayi Alhaji Abubakar Bello, dake karamar hukumar Sarkin pawa, ya gayawa wakilin Sashen Hausa Mustapaha Batsari cewa, an sace masa shanu 350, da tumaki 110. Haka nan barayin sun kona musu rumbun abinci kimanin 7. Wasu lokutan ma maharan sun bude rumbunan ne suka jefa wutan ciki don kona abincinsu ya kone.
Yanzu haka Alhaji Abubakar yace,ko abunda zasu ci basu da shi.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5