Garin Yanma dake Jihar Maradi a Niger Ya Samu Sabon Sarki

  • Ibrahim Garba

Sanusi Mamae Dan Bayaro, sabon sarkin Yanma

Bayan shekaru biyu da rasuwar sarkin Yanma Sabuwa dake cikin jihar Maradi a Jamhuriyar Niger, sabon zabe da aka gudanar, ya tabbatar da Sanusi Mamae Dan Bayaro a matsayin sabon sarki bayan ya kada abokin hamayyarsa Kadiri Gayya da kuri'a daya

Bayan kidaya kuri'un da aka kada Allah Ya zabi Sanusi Mamae Dan Bayaro ya zama sarkin Yanma Sabuwa a jihar Maradin Niger.

Sabon sarkin ya maye gurbin Sarki Mamman Gayya wanda ya rasu shekaru biyu da suka gabata.

Takarar zaben sarkin ta kasance ne tsakanin sabon sarkin ne da Kadiri Gayya wanda ya fadi da kuri'a daya. Kuri'u 30 aka kada amma daya bata da kyau saboda haka 29 aka kidaya. Sabon sarkin ya samu kuri'u 15 yayinda abokin hamayyarsa ya samu 14.

Gwamnan jihar Maradi Malam Zakari Umaru wanda ya gudanar da zaben shi ya bayyana sakamakon ya kuma tabbatar da sabon sarkin.

A karshen zaben sabon sarkin, Muryar Amurka ta ji ta bakin sarkin. Ya nuna farin cikinsa tare da yiwa Allah da jama'a da magabatan kasar godiya. Ya roki mutanensa da su taimaka masa su yi aikin kasa tare. Ya roki Allah ya taimakeshi ya rike adalci.

Shi ma dan takarar da ya fadi, Kadiri Gayya ya tofa albarkacin bakinsa tare da cewa shi mai hakuri na tare da Allah saboda haka komi a bar wa Allah.Shi ma, kamar sarkin ya godewa jama'a tare da cewa suna tare. Ya yi alkawarin goyon bayan sabon sarkin domin su ciyar da al'ummarsu gaba.

Talakawan garin sun nuna farin cikinsu da yiwa Allah godiya saboda sabon sarkin ya gaji kakansa da kuma mahaifinsa. Fatansu shi ne Allah ya taya sarkin riko ya ba garinsu ci gaba.

Ga karin bayani daga rahoton Mani Chuaibu.

Your browser doesn’t support HTML5

Garin Yanma dake Jihar Maradi a Niger Ya Samu Sabon Sarki - 2' 34"