Gargadi Kan Sabon Salon Damfara Ta Yanar Intanet A Najeriya

  • Ibrahim Garba

Ana ayyuka masu kyau da na barna ta yanar intanet

An ce karen bana maganin zomon bana. A yayin da 'yan damfara ta yanar intanet ke bullo da wau sabbin salo, haka su ma kungiyoyi da hukumomin da ke yaki da su ke bullo da sabbin matakan kama su.

Yawan damfarar mutane ta hanyar yanar intanet na karuwa a Najeriya, inda mutane kan yi asarar kudi da kuma ta kai ma a na biyan kudin fansa ta hanyar damfarar da ke da wuyar ganewa mai suna “BIT-COIN
Ibrahim Kyauka da Jamilu Muhammad na kungiyar yaki da ‘yan damfarar ta Najeriya sun bukaci jama’a su bullo da hanyar rufe layin wayar su da lambobin sirri don hakan ya hana samun bayanansu na boye in an sace masu waya ko kuwa in wayar ta bata.
Hakanan sun bukaci mutane su kauce wa amfani da ranar haihuwar su a matsayin lambar sirri ta katin daukar kudinsu na banki wato ATM.

Shin yaya hanyar hada-hadar kudi ta BIT-COIN ta ke aiki?.

Jamilu Muhammad ya ce rashin kwarewa ya sa a ka kama wani matashi da ya sace wata yarinya a Abuja da amsar diyya ta BIN-COIN.
Kazalika sun bukaci jama’a su guje wa bayyana asiran tafiye-tafiyensu ta kafofin sada zumunta don kauce wa sharrin miyagun iri.

Your browser doesn’t support HTML5

Sabon Salon Damfara Ta Yanar Intanet