Gareth Southgate Zai Jagoranci Tawagar Ingila Zuwa Italiya

Kasar Ingila ta tabbatar da cewar zata buga wasan sada zumunci tsakanita da kasar Italiya, kar karshin jagorancin kocinta Gareth Southgate.

Za'a yi wasanne a ranar 27 ga watan Maris na shekara mai kamawa 2020, a filin wasa na Wembley.

Ingila ta ce wannan wasa na daga cikin shirye-shiryen ta domin tunkarar gasar cin kofi na kasashen Turai Euro 2020, kana shine na farko cikin wasannin hudu na sada zumunci da zata yi domin tun karar gasar kasashen turai.

Inda a ranar 31 ga watan Maris zata barje gumi da Denmark, wanda za ayi a filin wasa na Wembley, haka zalika zata fafata da kasar Austria a ranar 2 ga watan Yuni, sai kuma Romania ranar 7 ga watan ta Yunin 2020.

Wannan ne karo na 28 da kasar Ingila zata fafata da Italiya, na baya-bayan nan shine aka tashi 1 da 1 a shekarar 2018 a Wembley.