Gyaran Fuska Ga Tsarin Ilmi Zai Taimakawa Matasa-FOMWAN

Matan kungiyar Musulmi ta FOMWAN reshen jihar Sokoto.

Kungiyar ta Mata Musulmi Tayi Wannan kiran ne a taronta na kasa karo na 18 da tayi a karshen mako a Jos jihar Flato.

Kungiyar Mata Musulmi ta Najeriya, wacce ake kira FOMWAN a takaice, tayi kiran da ayi garambawul ga harkokin ilmi a Najeriya, domin magance matsalolin rashin ayyukan yi da matasa da yaran kasar suke fuskanta.

Kungiyar tayi wannan kiran ne a taron ta na kasa karo 18 da tayi a Jos fadar Jahar Flato.

Kungiyar ta lura da cewa, karancin malamai kuma kwararru, da kayan aiki, da rashin ware kudi masu yawa domin harkar ilmi, da kuma ita kanta manhajar karatun, suna daga cikin matsaloli dake hana ruwa gudu ta fuskar ilmi.

Dr. Sumayya Hamza, kakakin kungiyar FOMWAN, ta bayyana takaicin kungiyar ganin yadda harkar ilmi ya tabarbare a kasar.

Kungiyar tayi kira ga masu ruwa da tsaki su tashi haikan wajen magance matsalar zauna gari banza bisa dalilai daban daban. Wadanda kungiyar tace za’a iya taimaka musu har su ma su taimakawa al’uma.

Mata daga jihohin Najeriya 36 ne suka halarci taron.

A saurari rahoton Zainab Babaji.

Your browser doesn’t support HTML5

Taron Kungiyar Mata Musulmi FOMWAN 3'19"