Hakan ya biyo ne bayan karatu na uku da ‘yan majalisar dokokin jihar suka yi wa daftarin dokar da gwamnan ya gabatar, bayan hukuncin babbar kotun Kano wadda ta rushe tsohuwar dokar da ta kafa masarautun hudu na Bichi, Gaya, Rano da Karaye da aka yi a watan Mayun da ya gabata.
Tanadin sabuwar dokar ya kumshi samar da majalisar sarakuna ta jihar Kano da shugabancin ta zai rinka jujjuyawa tsakanin sarakunan, kana da kuma hanyoyin kudaden tafiyar da ayukan masarautun na yau da kullum.
Shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin Kano Labaran Abdul Madari ya ce ba wani karin kashe kudi da karin masarautun zai haifar, domin kuwa kudaden da kananan hukumomi ke bayarwa bisa doka, su ne za’a ci gaba da rarrabawa ga masarautun gwargwadon yawan kananan hukumominsu.
Jama’ar jihar Kanon na bayyana ra’ayoyi mabambanta a kan lamarin. Yayin da wasu ke murna da ganin cancantar matakin, wasu ko na ganin akasin haka.
Da wannan sabuwar dokar, yanzu akwai sarakuna masu daraja ta daya guda biyar kenan a jihar Kano.
G karin bayani:
Your browser doesn’t support HTML5