Da yake karin haske kan matakin da gwamnati ta dauka Kwamishinan labaran jihar Neja, Mista Jonathan Batsa, ya ce gadajen dake unguwar baki ‘dayansu mallakar gwamnatin jiha ne, haka kuma unguwar ta zamanto mafakar barayi da masu garkuwa da mutane don kudin fansa.
A baya dai unguwar ta zamanto Barikin Soja, bayan da sojoji suka tashi ne gwamnatin jihar Neja ta sayi barikin daga hannu hukumar Soja. Bayan tashin sojoji mutane suka fara tarewa a gidajen dake Barikin, suka zauna har tsawon shekaru ba tare da ana karbar kudin haya daga gare su ba.
Kamar yadda Kwamishinan labaru Mista Jonathan Batsa, ya ce “yanzu gwamnati ta na bukatar gurin nan domin za a zo ayi abin da zai amfani jama’ar jihar baki ‘daya.”
Wakilin Muryar Amurka Mustapha Nasiru Batsari, ya ziyarci unguwar tsohuwar Barikin inda ya tarar da mutanen da wannan lamari ya rutsa da su na aikin kwashe sauran kayayyakinsu.
Adamu Mohammad wani mazaunin unguwar yace yanzu bai san inda zai tafi ba, wanda yayi ikirarin cewa an haifeshi a unguwar shekaru arba’in da bakwai, ya kuma ce gidajen iyayensu ne ba na gwamnati ba.
Dayawa daga cikin mutanen da gwamnati ta kora daga gidajen sun karyata maganar cewa an basu lokaci domin su kwashe kayayyakinsu su tashi daga gidajen.
Rahotanni na cewa yanzu haka motar rusau ta ruguje gidaje sama da dubu daya, haka kuma wani mutum daya da jariri sun rasa rayukansu lokacin da aka ruguza gidan da suke ciki.
Domin karin bayani saurari rahotan Mustapha Nasiru Batsari.
Your browser doesn’t support HTML5