Gamayyar Kungiyoyin Mata Musulmi, FOMWAN, Kan Polio

FOMWAN a Jihar Borno tana fadakar da iyaye muhimmancin yi wa 'ya'yansu rigakafin kamuwa da cutar Polio, ko shan inna
Babbar laimar kungiyoyin mata Musulmi a Najeriya, FOMWAN, reshen Jihar Borno, tana tallafawa membobinta da sauran jama'ar Jihar wajen gudanar da tarurrukan fadakarwa ko janyo hankali ga muhimmancin yi ma 'ya'yansu rigakafin kamuwa da muguwar cutar nan ta Polio mai nakkasawa ko ma kisa.

Da take magana a wurin wani taron da VOA da kuma Cibiyar yaki da Cututtuka Masu yaduwa ta Amurka suka shirya a Maiduguri, sakatariya ta Kungiyar FOMWAN a Jihar Borno, Malama Asabe Ali Komblon, ta ce a bayan wannan rigakafi na Polio ma, su na jaddada muhimmancin karbar sauran magungunan rigakafi ga iyaye da jama'ar gari.

Ta ce rassan kungiyar FOMWAN a dukkan kananan hukumomi 27 a Jihar Borno, su kan tara mata su yi musu nasiha, kan su mayarda hankali sosai domin idan rigakafin nan ya zauna a jikin yaro, to zai tashi cikin koshin lafiya ta yadda iyayensa ba zasu rika jelen zuwa asibiti ba.

Your browser doesn’t support HTML5

Malama Asabe Ali Komblon Ta FOMWAN A Borno Kan Gangamin Polio - 2:56