A wani taron manema labarai yau laraba, gamayyar kungiyoyin sun yaba da yadda zaben ya gudana babu tarzoma a sassan jihar Kano da kuma yadda galibin masu zabe suka bi doka da oda, amma sunyi tsokaci dangane da wasu al’amura da suka lura dasu kuma suke bukatar kulawar gaggawa gabanin zaben gwamnoni da na ‘yan Majalisun Dokoki na jihohi da zai wakana kasa da makonni biyu masu zuwa.
Comrade Mustafa Muhammad, ya nuna takaicinsa kan wasu abubuwa da masu saka ido a zaben suka kula da su, kuma suke bukatar kulawar gaggawa.
Hajiya Halima Ben Omar dake zaman sakatariyar kwamitin ta fayyace shawarwarin da kungiyoyin suka fitar a rahotan su domin daukar matakan gyara.
Dangane da banbancin dake tsakanin zaben shugaban kasa na shekara ta 2015 da kuma na bana, kungiyoyin kishin al’umar na Kano na cewa nasarar da aka samu a zaben 2015 kamata ya yi a wannan shekarar a samu wadda ta fita, amma maimakon hakan sai koma baya da aka samu.
Domin samun cikakken labarin saurari rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.
Your browser doesn’t support HTML5