Ga Yadda Wasan Zakarun Turai Zai Kasance A Bana

Bayan kammala wasan rukuni na gasar cin kofin duniya ajin Mata na shekarar 2019, da akeyi a kasar Faransa, yanzu haka an fidda jaddawalin wasan zagaye na 16 mai taken kifuwa daya kwala (Nock Out).

Inda tawagar kwallon kafa ta Najeriya Super Falcons ta samu tsallakawa zagaye na gaba. Najeriya ta samu gurbin ne bayan da Chile ta kasa
doke Thailand 3-0, inda suka tashi wasa Chile taci 2-0.

Hakanne yasa Super Falcons ta zama kungiya ta karshe da ta cike gurbin kungiyoyi 16 da za su fafata a wasannin zagaye na biyu.

Ga kuma yadda Jaddawali yake: Jamani da Najeriya, Norway da Australia, sai kuma kasar Ingila da Kamaru, Faransa mai masaukin baki zasu fafata da Brazil, Spain da Amurka, Sweden da Canada, Itali da China da kuma Netherlands da Japan.

Za'a fara wasannin zagaye na biyu ne ranar Asabar 22 ga watan Yuni 2019, tsakanin Jamani da Najeriya da misalin karfe hudu da rabi na yammacin agogon Najeriya, Nijar da Kamaru, sai kuma da misalin karfe takwas Norway da Australia.