Trump dai ya shafe kusan minti biyar yana jawabi a lokacin da aka fara jin harbe harben. An ga Trump ya taba kunnensa na dama sannan ga wani abu kamar jini a fuskarsa, kafin jami’an leken asiri su ka sa ya duke.
Trump yana kan nuna wasu alkaluma na baki da ke tsallako iyakar kasar ne aka ji karar harbe harben a wurin taron.
Nan take jami'an ba da kariya suka garzaya zuwa wurinsa kuma an ci gaba da jin karar harbin yayin da jami’an ke kula da Trump.
A cikin wata sanarwa da ya fitar daga baya, kwamitin yakin neman zaben Trump ya ce tsohon shugaban na nan lafiya.
"Shugaba Trump ya godewa jami'an tsaro da masu aikin gaggawa saboda matakin da suka dauka ba tare da bata lokaci ba a lokacin da lamarin ya faru," a cewar kakakin kwamitin Steven Cheung a cikin sanarwar.
Hakazalika a wata sanarwa da hukumar leken asiri ta fitar, ta ce "Tsohon Shugaban yana cikin koshin lafiya."