A jiya ne hukumar kare farar hula wadda aka fi sani da cilvil defence suka kama wani dan shekara talatin da biyu da haihuwa kanlaifin yi wa wata yarinya fyade, har ma ya yi mata ciki.
Dr Muhammed Gidado shine kwamandan hukumar tsaro da kare al'uma ta kasa a jahar Jigawa, kuma daya daga cikin matsalolin da suke fama da su a Jahar ita ce yawan fyade da ake yi wa yara mata a wurare daban daban. Shugaban ya yi bayani akan wani mutum da ya yi wa wata yarinya fyade a karamar hukumar Kazaure.
"mun kama shi ne a sakamakon fyaden da yayi wa wata yarinya kuma har ma ay yi mata ciki, kuma irin wadannan matsalolin suna da yawa ba ma a Jahar jigawa kadai ba kusan ko ina a Najeriya hakan na faruwa. Amma abin jin dadin anan shine irin kokarin da alkalai ke yi, ko watan da ya wuce mun kai wani wanda yake wa dalibar shi fyade a bayan daki".
Daga karshe babban jami'in ya yi bayanin cewa yawancin masu fyaden dai suna fadar cewa bokayen su ne suka ba su shawarar yin hakan domin warkewa daga wata cuta.
Ga karin bayani.