Rundunar 'yan sanda jihar Filato ta bayyana damuwa kan yawaitar fyade da ake wa kananan yara a jihar.
WASHINGTON DC —
Kwamishinan 'yan sandan jihar Undie Adie ya bayyanawa manema labarai cewa, a cikin watanni biyu, rundunar ta samu karin kararrakin fyade sau 19 kuma cafke mutane 24 da ake zargin aikatawa.
Kungiyar 'yan jarida mata ta shirya gangamin fadakar da jama'a kan yaki da cin zarafin yara da yin fyade.
Shugabar kungiyar reshen jihar Filato, Madam Jennifer Yarima, ta bayyana cewa, a kusan kowace rana suna samun rohoton fyade.
"Mun fito ne don mu gayawa duniya cewa ba mu yarda da fyade ba domin mun gane cewa abun sai karuwa ya ke, ana yi wa yaranmu da mata fyade ko gonaki, ko a gidaje ko a makarantu. "
Saurari cikakken rohoton Zainab Babaji
Your browser doesn’t support HTML5