Sakamakon kalamun da Aisha Alhassan ministar harkokin mata ta yi na cewa idan Atiku Abubakar da Shugaba Muhammad Buhari suka tsaya takarar shugaban kasa a shekarar 2019 za ta goyi bayan Atiku Abubakar ya sa mazauna jihar Oyon Najeriya mai da martani.
Malam Umaru Lamido yana mai cewa Aisha ta fadi ra'ayinta. Ta kuma nuna cewa ta fita goyon bayan Shugaba Buhari. Duk da cewa tana son a ce ita ba munafuka ba ce amma ta nuna bangaranci a kalamunta. Lamido na ganin furucinta ya nuna jam'iyyar APC za ta dare gida biyu. Shugaba Buhari da nashi bangaren kana Atiku Abubakar da nashi.
Ita ko Hassana daga Maniya cewa ta yi Aisha ta yi buturci ta zama bakin kaza. Buhari ne ya nada ta minista. Shi ya daure mata gindi ta zama abun da ta zama. Amma furucinta ya nuna buturu ce. "Mu mata ma bamu san aikinta ba" inji Hassana.
A cewar Hassana Najeriya bata son munafuki a mulkin Buhari kuma ba na munafuki ba ne. Wai "Buhari ya dauketa yana cewa diya ce alhali kuwa ba diya ce ba" a cewar Hassana.
Hassana tace tana cikin wadanda suka kada mata kuri'ar zama gwamna. Tayi bakin cikin ba ta ci gwamnan ba amma sai gashi yanzu ta ce ba ta son Shugaba Buhari. Za ta zabi wani. Ke nan ta zama bakin kaza, inji Hassana.
Sa'adu Adamu na ganin furucin Aisha bukata ce ta rayuwa kuma abun ra'ayi ne. Yace tana ganin wajen Atiku ya fi mata.Ya yi tambaya ko akwai mai barin ubangidansa akan wani.
Mai Shadda daga Ibadan bai ga laifinta ba saboda tana iya yiwuwa ta san anfanin Atiku.
Ga rahoton Umar Hassan Tambuwal da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5