Kungiyar Miyatti Allah ta ce ba Fulani ne su ka kai hari a Miata da Izam na karamar Hukumar Anambara wanda ya yi sanadin mutuwar mutane shida da kuma raunata wasu kamar yadda ake zargi ba. Da yake karin haske kan matsayin na kungiyar Miyatti, shugaban kungiyar ta Miyatti Allah shiyyar kudu maso gabashin Najeriya, Alhaji Gidado y ace hasali ma abin da aka tabbatar ya faru shi ne ranar daya ga watan Janairu wasu natasan yankin sun zo sun far ma ‘ya’yan Fulani har su ka guntule masu kai kuma har an kama wdanda su ka aikata kuma su na gidan yari.
Ya ce bayan da aka samu kwanciyar hankali na wani dan lokaci kuma ranar tara ga watan Fabraru sai wasu mutane su ka kashe Fulani uku saboda an kashe wani mutum cikin daji kuma sun a kyautata zaton Fulani ne su ja aikata alhalin kuwa su kansu Ibo din su na tashin hankali da juna. Ya ce har yanzu ba a bar su sun kwashi gawarwakin wadanda su ka mutu din ba. Ya ce tun sannan Fulanin garin sun bar Anambara West. Malam Ardo ya ce hatta garin da Fulanin su ka gudu su ka je an bi su don a kai masu hari amma wasu ‘yan garin su ka gaya wa Fulanin su gudu, kuma su ka gudu.
Da Muryar Amurka ta tuntubi Rundunar ‘yansandan jahar ta Anambara ta wanke Fulani daga zargin. Kwamishinan ‘Yansandan jahar Alhaji Mustapha Dandaura y ace zargin da ake wa Fulani ba daidai ba ne. Y ace akwai kungiyoyin asiri da keg aba da juna wadanda ake kyautata zaton su ne su ka kashe mutanen.
Ga dai wakilinmu Alphonsus Okoroigwe da cikakken rahoton: