Yanzu haka, dokar hana kiwo da wasu jihohi a arewacin Najeriya suka soma aiwatarwa,ya soma jefa makiyaya da dabbobin su cikin wani mawuyacin hali da ka iya shafan tattalin arziki.
Kama daga jihar Binuwai, Nasarawa zuwa Taraba da Adamawa kawo yanzu akwai daruruwan Fulani makiyayan da ke cikin mawuyacin hali sakamakon tashe tashen hankulan dake faruwa.
Wasu makiyayan cewa suke dabbobinsu na mutuwa sabili da kona wuraren kiwon da aka yi musamman a jihar Binuwai da Taraba inda aka soma aiwatar da dokar hana kiwo,kamar yadda wannan makiyayin ya shaidawa wakilin Muryan Amurka Ibrahim Abdulazeez
Kungiyarta makiyaya tace muddin gwamnati bata tashi tsaye ba,to fa labudda kasar ka iya fadawa wani halin tashin hankali da kuma tattalin arziki.
Dr Aliyu Tilde na kungiyar Fulbe Global wanda da shi aka zaga wasu wuraren da lamarin ya shafa musamman a jahar Banuwai,ya bayyana abun da suka gani da kuma halin da ake ciki.
Ga Ibrahim Abdulazeez da Karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5