Fulani Nada Rawar da Zasu Taka a Siyasar Najeriya

Shugaban Fulani makiyaya Haruna Usman.

Suma al’uma Fulani ba a barsu a baya ba wajen kira ga daukacin ilahirin Fulani a ko ina, da su guji tada zaune tsaye. Sakataren kungiyar “Miyetti Allah” ta kasa Baba Usman Galdama, yayi wannan kiran a madadin kungiyar ta kasa. Yace kungiyar su ta na da mambobi kimanin miliyan 20 a cikin Najeriya, don haka suma suna da rawar da zasu taka wajen ciyar da kasar gaba.

Yayi kira da diyan makiyaya a ko ina suke su guji tada hankulan a’umah kuma kada su bari ayi amfani da su wajen muzguna ma wasu, don cinma wani buri nasu. Ya kuma kara da cewar duk inda Fulani suke su bama wannan zababbiyar gwamnatin goyon baya dari bisa darin don tasamu ta aiwatar da duk abubuwan ciyarda kasa gaba.

Su dai babban burin su shine, suga wannan gwamnatin tasamu hadin kan ‘yan kasa da kuma kawo cigaba a kowane mataki. Don haka suna kira da babbar murya, cewar duk inda Fulani, duke suyi kokari su fita suje wajen zabe don kada kuri’arsu a wannan zaben me zuwa idan Allay a kaimu ranar Asabar me zuwa.